Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ƙayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuɓar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Date | Title & Description | Contributors |
---|---|---|
2025-02-18 | Shirin ya duba matakin gwamnatoci na sahale wa kafa Jami'oi masu zaman kansu bisa sharuda da ka'idoji domin bayar da ci-gaban ilimi a Najeriya. |
|
2025-02-11 | Ko kun san wani abun busa da aka fi amfani da shi a gidajen sarauta wato "kakaki", ku biyo mu cikin Shirin Taba Ka Lashe. |
|
2025-01-21 | Shekaru aru-aru maroka da mawakan baka na bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunkasa al'adu da martaba kimar al'umma a daular Hausa. |
|
2025-01-14 |
|
|
2025-01-07 | Ko kun san cewa har yanzu ana gudanar da al-adar nan ta sayen baki a Kasar Hausa idan an yi aure? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai. |
|
2024-12-10 | Tsarin karatun Allo na neman ilimin da gwamnatin jihar Borno a Najeriya ke kokarin kyautatawa |
|
2024-12-03 | Shirin na al'adu ya duba tasirin gidan tarihi na Arewa (Arewa House) da ke Kaduna da ya tattara tarihin Marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da al'adu da sana'o'in yankin Arewacin Najeriya. |
|
2024-11-26 | Shirin ya duba al'adar kacici-kacici ko wasa kwakwalwa da malam Bahaushe ke amfani da ita wajen ilimantawa. |
|
2024-11-12 | Shirin ya mayar da hankali ne kan masarautar Wurkun da ke karamar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya, |
|
2024-11-06 | Shirin ya duba al'adar Masquerade, ko Basaje kamar yadda ake fassarawa, da ta kafu a yankin Kabilar Igbo a Najeriya. |
|